-
Kamfanin Boeing Ya Amince Ya Dakatar Da Ayyukan Jirginsa Samfurin 737 Max - 8
Mar 15, 2019 16:46Kamfanin kera jirage na Boeing na kasar Amurka ya amince ya dakatar da ayyukan jirginsa samfurin 737 Max - 8, biyo bayan hatsarin da ya auku da jirgin a kasar Ethiopia a cikin wannan mako.
-
Wani Jirgin Fasinja Yayi Hatsari A Kasar Indunisya Dauke Da Fasinjoji
Oct 29, 2018 05:55Rahotanni daga kasar Indunisiyya sun bayyana cewar wani jirgin saman fasinja samfurin Boeing 737 dauke da mutane 188 yayi hatsari a cikin teku jim kadan bayan ya tashi da birnin Jakarta, babban birnin kasar Indunusiya.
-
Sudan: An Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Sama A Khartum
Oct 04, 2018 08:03Wasu jiragen sama biyu ne su ka yi taho mu gama a filin saukar jirage na birnin Khartum wanda hakan ya kawo tsiko a zirga-zirgar jirage
-
Hatsarin Jirgin Sama Ya Ci Rayukan Mutum 20 A Sudan Ta Kudu
Sep 09, 2018 19:18Hukumomin Kasar Sudan Ta Kudun sun sanar da mutuwar mutum 20 sanadiyar hatsarin jirgin saman fasinja a Juba babban birnin kasar
-
Wani Jirgin Daukar Kayan Rasha Yayi Hatsari A Siriya, Mutane 32 Sun Mutu
Mar 06, 2018 16:37Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta bayyana cewar wani jirgin saman daukar kaya da rundunar sojan kasar suke amfani da shi ya fado a kasar Siriya, inda alal akalla mutane 32 da suke cikin jirgin suka mutu.
-
Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Ayyukan Binciken Jirgin Saman Da Ya Fado A Iran
Feb 19, 2018 11:03Mahukunta a kasar Iran sun bayyana cewar an tura sama da kwararrun hawa duwatsu 100 tare da wasu jami'an ba da agaji da dama yankin da ake tsammanin jirgin saman daukar fasinjoji na kasar ya fadi a jiya don ci gaba da bincike da gano buraguzan jirgin duk kuwa da matsalar rashin kyawun yanayi da ake fuskanta.
-
Kasar Katar Ta Kai Karar Saudiyya A gaban Majalisar Dinkin Duniya
Aug 20, 2017 18:13Karar da Kasar ta Katar din ta shigar ta shafi barazanar da Saudiyyar ta yi na harbo jiragen fasinjanta.
-
An gano wasu shaidun ta'addanci a jiragen kasar Masar
Dec 16, 2016 06:28A farkon tsakiyar shekarar 2016 Jiragen Masar sun fadi dalilin harin ta'addanci.
-
Hatsarin Jirgin Sama Ya Hallaka Wasu 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Brazil
Nov 29, 2016 16:37Mahukunta a kasar Kolombiya sun bayyana cewar mutane shida ne kawai suka tsira bayan da wani jirgin sama dauke da mutum 81 masu buga wa wani kulob din kwallon kafa na kasar Brazil ya fado a kusa da birnin Medellin na kasar a yau din nan Talata.
-
Wani Jirgin Saman Kamfanin Emirates Yayi Hatsari Dauke Da Mutane 275
Aug 03, 2016 11:16Kamfanin jiragen saman Emirates na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ya sanar da cewa wani jirgin saman kamfanin dauke da fasinjoji da ma'aikata 275 yayi hatsari a filin jirgin saman Dubai