Wani Jirgin Fasinja Yayi Hatsari A Kasar Indunisya Dauke Da Fasinjoji
(last modified Mon, 29 Oct 2018 05:55:13 GMT )
Oct 29, 2018 05:55 UTC
  • Wani Jirgin Fasinja Yayi Hatsari A Kasar Indunisya Dauke Da Fasinjoji

Rahotanni daga kasar Indunisiyya sun bayyana cewar wani jirgin saman fasinja samfurin Boeing 737 dauke da mutane 188 yayi hatsari a cikin teku jim kadan bayan ya tashi da birnin Jakarta, babban birnin kasar Indunusiya.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya jiyo kakakin Hukumar bincike da agaji ta kasar Indunusiya Yusuf Latif yana fadin cewa jirgin saman wanda yake kan hanyarsa ta zuwa garin Pangkal Pinang, inda yayi hatsari cikin tekun. Jami'in kara da cewa cibiyar da ke kula jigilar jiragen saman sun rasa hanyar sadarwa da jirgin jim kadan bayan tashinsa.

Jami'an kasar Indunisiyan sun ce jirgin saman yana dauke da mutane 188, cikinsu akwai manyan mutane 178, karamin yaro guda da kuma wasu jarirai biyu, bugu da kari kan matukan jirgin guda 2 da kuma ma'aikatan jirgin su 5. Jami'an sun kara da cewa har ya zuwa yanzu dai ba a da tabbacin ko akwai wadanda suka tsira da rayukansu cikin jirgin.

Ana ci gaba da gudanar da bincike don gano jirgin da mutanen da suke cikinsa.