Sojan Saman Nijeriya Guda Ya Rasu Sakamakon Hatsarin Jirgi A Abuja
(last modified Sat, 29 Sep 2018 05:56:50 GMT )
Sep 29, 2018 05:56 UTC
  • Sojan Saman Nijeriya Guda Ya Rasu Sakamakon Hatsarin Jirgi A Abuja

Rundunar sojin saman Nijeriya ta sanar da cewa daya daga cikin matuka jiragen samanta guda biyu da suka yi hatsari a wata unguwa a birnin tarayya Abuja a daidai lokacin da suke shawagi cikin shirye-shiryen bukukuwan ranar 'yancin kai da za a gudanar nan gaba.

A wata sanarwa da rundunar sojin sama ta Nijeriya ta fitar dauke da sanya hannun mai magana da yawunta, Ibikunle Daramola, ta ce wasu jiragen saman rundunar sojin saman ta Nijeriya samfurin F-7Ni da suke gudanar da shawagi a shirye-shiryen da ake yi don gudanar da bukukuwan shekaru 58 da samun 'yancin kai sun yi hatsari a ranar 28, Satumba, 2018.

Sanarwar ta kara da cewa hatsarin ya tilasta wa matuka jiragen su 3 ficewa daga jirgin inda daga baya ya fadi a dutsen Katamkpe. Sanarwar ta kara da cewa abin bakin cikin shi ne cewa daya daga cikin matuka jirgin ya rasa ransa sakamakon raunukan da ya samu.

Rahotanni sun ce sojan da ya rasa ran nasa shi ne Sqn Ldr Baba Ari wanda aka bayyana shi a matsayin hazikin soji mai kwazo wajen aikinsa.

Babban hafsan hafsoshin sojin sama na Nijeriyan, Air Marshal Sadique Abubakar ya isar da sakon ta'aziyyarsa ga iyalai da 'yan'uwan sojan da ya rasa ran nasa.