Mar 15, 2019 16:46 UTC
  • Kamfanin Boeing Ya Amince Ya Dakatar Da Ayyukan Jirginsa Samfurin 737 Max - 8

Kamfanin kera jirage na Boeing na kasar Amurka ya amince ya dakatar da ayyukan jirginsa samfurin 737 Max - 8, biyo bayan hatsarin da ya auku da jirgin a kasar Ethiopia a cikin wannan mako.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, bayan wata doguwar tatatunawa tsakanin manyan jami'an kamfanin Boeing da kuma jami'an hukumar kula da lafiyar jiragen sama  akasar Amurka, da kuma wasu manyan kamafanoni masu aiki da jirage kera  a duniya, kamfanin ya amince ya dakatar da dukkanin ayyukan jirgin nasa samfurin 737 Max - 8 da ya yi hadari.

Amma duk da amincewar da kamfanin ya yi da hakan, ya kuma bayyana cewa yana tabbaci kan jirgin nasa da kuma ingancinsa, domin kuwa an gudanar da sabbin ayyuka na zamani a cikin tsarin jirgin, to amma sakamakon matsalolin da aka samu a cikin lokutanan kamfanin ya amince da kiraye-kirayen da aka yi masa.

A ranar Lahadi 10 ga wannan wata na Maris ne dai jirgin Boeing 737 Max - 8 mallakin kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Ethiopian Airlines ya yi hadari a birnin Addis Abba jima kadan bayan tashinsa, inda dukkanin mutane 157 da suke cikin jirgin suka rasa rayukansu, lamarin da ya sanya wasu daga cikin kasashen duniya sanar da cewa sun dakatar da yin amfani da jirgin, da kuma rufe sararin samaniyarsu ga wannan samfurin jirgi.

Tags