Hatsarin Jirgin Sama Ya Ci Rayukan Mutum 20 A Sudan Ta Kudu
(last modified Sun, 09 Sep 2018 19:18:10 GMT )
Sep 09, 2018 19:18 UTC
  • Hatsarin Jirgin Sama Ya Ci Rayukan Mutum 20 A Sudan Ta Kudu

Hukumomin Kasar Sudan Ta Kudun sun sanar da mutuwar mutum 20 sanadiyar hatsarin jirgin saman fasinja a Juba babban birnin kasar

Kafar watsa labaran Annashra ta nakalto hukumomin kasar Sudan ta kudu na cewa a wannan Lahadi wani jirgin sama na Fasinja da ya tashi daga birnin Juba a kan hanyarsa na zuwa garin Yirol ya yi hatsari inda ya fadi cikin wani tabki dake gefen birnin na Juba, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 20

Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana dalilin hatsarin ba, saidai hukimomin kasar Sudan ta kudun sun ce tuni aka fara gudanar da bincike domin gano musababin hatsarin.

A cewar jaridun kasar sudan ta kudun, daga cikin wadanda hatsarin ya ritsa da su akwai wani likita dan kasar Italiya da wani malamin addinin kirista.