Pars Today
Ma'ikatar harkokin wajen kasar Iran ta kirayi jakadiyar kasar Kenya a Tehran, domin nuna rashin jin dadi kan hukuncin da wata kotun Kenya ta fitar ci gaba da tsare wasu Iraniyawa biyua kasar ta Kenya.
A jiya Asabar ne kasar ta Kenya ta kirayi jakadanta Lucas Tumbo daga Magadishu bisa sabanin da ya kunno kai a tsakanin kasashen biyu akan iyakokin ruwa
Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyata, ya sanar da kawo karshen harin da wasu 'yan bindiga suka kai a wani Otel dake Nairobi babban birnin kasar, bayan shafe kusan sa'o'i 20 ana fafatawa da maharan.
Kungiyar Al-shebab ta dauki alhakin kai wani hari data ce mayakan ta ne suka kai shi a Nairobi babban birnin kasar.
Alkalin wata babban kotu a kasar Kenya ya tabbatar da laifin kisa kan wani tsohon jami'in 'yansanda na kasar, hukuncin da kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka yi na'am da shi.
Shugaban kasar Kenya ya sanar da cewa: Sojojin kasarsa zasu ci gaba da aikin wanzar da zaman lafiya a Somaliya har zuwa lokacin da za a samu kwanciyar hankali a kasar.
An zargi gwamnatin kasar Kenya da tsaurara matakai a kan 'yan gudun hijira na kasashen ketare da suke a cikin kasarta.
Mahukunta a kasar Kenya sun kori wani dan kasar China mai suna Liu Jiaqi daga kasar bayan wani faifan bidiyo da yayi kuma ya watsa yana bayyana al'ummar kasar ciki kuwa har da shugaba Uhuru Kenyatta a matsayin birrai.
Ana samun ci gaba ta fuskar habbar harkokin kasuwanci tsakanin kasashen Iran da kuma Kenya.
Majalisar musulmin kasar Kenya ta nuna matukar damuwa dangane da karuwar ayyukan cin hanci da rashawa a kasar.