Sojojin Kenya Zasu Ci Gaba Da Kasancewa A Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33635-sojojin_kenya_zasu_ci_gaba_da_kasancewa_a_somaliya
Shugaban kasar Kenya ya sanar da cewa: Sojojin kasarsa zasu ci gaba da aikin wanzar da zaman lafiya a Somaliya har zuwa lokacin da za a samu kwanciyar hankali a kasar.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Oct 15, 2018 12:18 UTC
  • Sojojin Kenya Zasu Ci Gaba Da Kasancewa A Somaliya

Shugaban kasar Kenya ya sanar da cewa: Sojojin kasarsa zasu ci gaba da aikin wanzar da zaman lafiya a Somaliya har zuwa lokacin da za a samu kwanciyar hankali a kasar.

Kamfanin dillancin labaran China na Xin Huwa ya watsa rahoton cewa: Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ce rundunar sojin Kenya da suke aikin wanzar da zaman lafiya da sulhu a Somaliya zasu ci gaba da zama a cikin kasar har zuwa lokacin da za a samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Kenyatta ya jaddada cewa: Rundunar sojin kasarsa ta Kenya Defence Forces suna cikin kasar Somaliya tun daga shekara ta 2011, kuma zasu ci gaba da zama har zuwa lokacin da za a samu cikakken zaman lafiya a kasar.