An Samu Habbakar Harkokin kasuwanci Tsakanin Iran Da Kenya
Ana samun ci gaba ta fuskar habbar harkokin kasuwanci tsakanin kasashen Iran da kuma Kenya.
Kamfanin dillancin labaran Mehr ya bayar da rahoton cewa, jakadan kasar Iran a kasar Kenya Hadi faraj Wand ya fadi a jiya Laraba cewa; shekaru biyu da suka gabata harkokin kasuwancin da ke tsakanin Kenya da Iran bai wuce dala miliyan 39 a cikin shekara ba, amma a wannan shekara ya kai dala miliyan 200, kuma akwai yiwuwar nan da wani lokaci zai kai dala miliyan 500.
Jakadan na Iran a kasar Kenya ya ce, dukkanin kasashen biyu suna da dama da ya kamata su yi amfani da ita ta fuskoki da dama domin bunkasa harkokin kasuwanci da cinikayya da ke tsakaninsu, musammana bangarorin saka hannayen jari a tsakanin kasashen biyu.
Kasar Kenya tana daga cikin kasashen gabashin nahiyar Afrika da suke da kyakkyawar dangantaka ta diblomasiyya tare da kasar Iran.