Pars Today
Rundunar sojin Masar ta sanar da kashe wasu 'yan ta'adda 18 a yankunan da suke lardin Sina da ke shiyar arewa maso gabashin kasar.
Wata kotu a birnin Alkahira na kasar Masar ta sanya sunayen 'yan kungiyar Ihwanul-Muslimin 164 cikin jerin sunayen 'yan ta'adda a kasar.
Wata kotu a birnin Alkahira ta kasar Masar ta sanya sunayen wasu mutane 164 daga cikin jagororin kungiyar 'yan'uwa musulmi ta Muslim Brotherhood ta kasar cikin jerin sunayen 'yan ta'adda.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Masar ce ta sanar da cewa an kashe 'yan ta'addar ne a tsakiyar kasar
Majiyar labarai daga kasar masar sun bayyana cewa gwamnatin kasar ta kuduri aniyar aikewa da sojojin kasar zuwa kasar Libya.
'Yan sandan Masar sun kama wani masanin harkar tattalin arziki kuma marubuci kan zargin sukar mahukuntan kasar kan gazawa a fagen inganta harkar tattalin arzikin kasar.
Shugaban kasar Masar Abdul Fattah al-Sisy ne ya sanar da tsawaita aiki da dokar ta bacin na tsawon watanni uku
Wata kotu a Masar ta yanke hukuncin kisa kan mutane uku da kuma dauri a gidan kurkuku kan wasu ashirin na daban kan laifin ayyukan ta'addanci.
Dan tsohon shugaban Majalisar Dokokin Masar ya zargi tsohuwar gwamnatin kasar karkashin shugabancin Husni Mubarak da aiwatar da kashe-kashen gilla kan masu sabanin ra'ayi da ita.
Kwamitin kula da zabuka a kasar Masar ya sanar da cewa: Suna ci gaba da tantance sunayen mutanen da suka ki kada kuri'a a zaben shugaban kasa da aka gudanar a Masar da nufin mika su ga ma'aikatar shari'ar kasar.