Masar : An Yanke Hukuncin Kisa Kan Wasu Mutane
Wata kotu a Masar ta yanke hukuncin kisa kan mutane uku da kuma dauri a gidan kurkuku kan wasu ashirin na daban kan laifin ayyukan ta'addanci.
Rahotonni daga Masar sun bayyana cewa: Kotun da ke shari'ar manyan laifuka ta birnin Alkahira a yau Lahadi ta yanke hukuncin kisa kan wasu mutane uku da kuma dauri kan wasu mutane 20 na daban kan laifuka da suka shafi ayyukan ta'addanci da kuma kafa kungiyar 'yan ta'adda mai suna Kata'ib Ansarus-Shari'ah.
Tun bayan da sojoji suka kifar da zababbiyar gwamnatin Muhammad Morsi a watan Yulin shekara ta 2013 a Masar aka fara samun bullar kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar, inda suke kai hare-haren wuce gona da iri kan jami'an tsaron Masar da kuma wajajen taruwar jama'a a kasar lamarin da ya janyo hasarar rayukan dubban mutane tare da jikkata wasu adadi mai yawa.