An Sake Tsawaita Lokacin Aiki Da Dokar Ta Baci A Kasar Masar
Shugaban kasar Masar Abdul Fattah al-Sisy ne ya sanar da tsawaita aiki da dokar ta bacin na tsawon watanni uku
Kafar watsa labarun al-Misriyyun, ta ambaci cewa; Dukkanin jami'an tsaron kasar za su kasance a cikin shirin ko-ta-kwana domin fuskantar barazanar tsaro da kasar ciki.
Tun a 2017 ne dai aka fara aiki da dokar ta baci a kasar, bayan wani harin ta'addanci da aka kai wa wasu majami'u biyu wanda ya yi rayukan mutane 45.
Duk bayan watanni uku dai ana sake jaddada aiki da dokar ta bacin a kasar ta Masar.
A karkashin tsarin mulkin kasar ta Masar. shugaban kasa yana da ikon sanar da kafa dokar ta baci bayan shawara da majalisa da kuma ministoci.
Masar tana fuskantar barazanar tsaro daga kungiyoyin 'yan ta'adda da su ka hada da masu alaka da Isis da kuma alka'ida.