Mahukuntan Masar Sun Kama Wani Masanin Harkar Tattalin Arzikin Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33736-mahukuntan_masar_sun_kama_wani_masanin_harkar_tattalin_arzikin_kasar
'Yan sandan Masar sun kama wani masanin harkar tattalin arziki kuma marubuci kan zargin sukar mahukuntan kasar kan gazawa a fagen inganta harkar tattalin arzikin kasar.
(last modified 2018-10-22T12:38:49+00:00 )
Oct 22, 2018 12:38 UTC
  • Mahukuntan Masar Sun Kama Wani Masanin Harkar Tattalin Arzikin Kasar

'Yan sandan Masar sun kama wani masanin harkar tattalin arziki kuma marubuci kan zargin sukar mahukuntan kasar kan gazawa a fagen inganta harkar tattalin arzikin kasar.

Rundunar 'yan sandan Masar a jiya Lahadi ta yi awungaba da Abdul-Khaliq Faruq marubuci kuma masanin harkar tattalin arziki kan zarginsa da yin maganganu marassa tushe kan halin tattalin arzikin kasar.

Kafin rundunar 'yan sandar Masar ta kama Abdul-Khaliq Faruq ta dauki matakin hana buga wani littafin da ya wallafa kan harkar tattalin arziki da ya kira littafin da cewa: "Shin Masar tabbas matalauciyar kasa ce?".