Pars Today
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteres, a'ummar Rohingyas dake gugun hijira a Bangaladesh.
A karon farko, cikin shekaru 50 Amurka ta rasa shugabancin hukumar kula da kaurar bakin haure ta Majalisar Dinkin Duniya, bayan da aka zabi dan Portugal, Antonio Vitorino, a matsayin sabon shugaban hukumar a yau.
Hukumar MDD dake kula da 'yan gudun hijira Falasdinawa, na neman tallafin kusan dala miliyan 250, don cike gibin kudaden da take bukata a bana.
Kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce yana shirin zabar mambar da zata maye gurbin AMurka, bayan da Amurkar ta fice daga kwamitin.
Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato majiyar MDD dangane da rahoton "Ci Gaba Mai Dorewa 2018" wanda ya ambaci gurbar yanayi da hatsarin da ke tattare da shi
Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin DUniya ce ta sanar da adadin 'yan gudun hijirar da ake da su a duniya
Yunkurin na Majalisar Dinkin Duniya, na ganin ta farfado da tattaunawar sulhu tsakanin masu rikici a Yemen, na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada a birnin Hodaida wanda ya kunshi tashar ruwa a yammacin kasar ta Yemen.
A daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada a kusa da filin jirgin sama na Hodeida, wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Yemen, na ci gaba da tuntubar masu rikici akan samar da hanyoyin kauce wa jefa mazauna yankin cikin mawuyacin hali.
Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai a kasar Yamen ya bayyana cewa: Tashar ruwan Hudaidah ce kawai ta rage a matsayar kafar shigar da kayayyakin jin kai zuwa cikin kasar Yamen.
Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya zabi kasashen Jamus, Belgium, Afirka ta Kudu, Jamhuriyar Dominica da kuma Indonusiya a matsayin sabbin membobin Kwamitin Tsaro na Majalisar na wa'adin shekaru biyu.