MDD Na Ci Gaba Da Tuntubar Masu Rikici A Yemen
A daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada a kusa da filin jirgin sama na Hodeida, wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Yemen, na ci gaba da tuntubar masu rikici akan samar da hanyoyin kauce wa jefa mazauna yankin cikin mawuyacin hali.
Yau dai kwana na biyar kenan da kawancen da Saudiyya ke jagoranta hadin gwiwa da hadaddiyar daular labarawa ya kaddamar da farmaki a yankin na Hodeida da nufin kwato shi daga hannun 'yan gwagwarmayar neman sauyi na Houtsis a Yemen.
Kaddamar da farmakin a birnin, wanda ya kunshi tashar ruwan Hodeida, kan iya jefe rayuwar fararen hula cikin tsaka mai yuwa, kasancewar ta nan ne ake shigar da yawancin kayan agajin da ake shigar dasu don taimakawa fararen hula a kasar ta Yemen.
MDD, dai ta yi kira da babbar murya da a dakatar da yaki a kasar ta Yemen, don lalubo hanyoyin samar da zaman lafiya ta hanyar siyasa.
A jiya ne dai wakilin MDD a kasar ta Yemen, Martin Griffiths, ya isa birnin Sanaa, inda yake ci gaba da ganawa da bangarorin dake rikici a kasar.