Karon Farko, Amurka Ta Rasa Shugabancin Hukumar OIM
(last modified Fri, 29 Jun 2018 17:39:13 GMT )
Jun 29, 2018 17:39 UTC
  • Karon Farko, Amurka Ta Rasa Shugabancin Hukumar OIM

A karon farko, cikin shekaru 50 Amurka ta rasa shugabancin hukumar kula da kaurar bakin haure ta Majalisar Dinkin Duniya, bayan da aka zabi dan Portugal, Antonio Vitorino, a matsayin sabon shugaban hukumar a yau.

Tun tashin farko ne dai akayi waje da dan takaran na Amurka, dake samun goyan bayan Shugaba Trump, cewa da Ken Isaacs, da ake zargi da nuna kyama ga bakin haure dama kin amauncewa da wasu halaye dake cilasta yin kaura kamar canjin yanayi.

Nasara Mista Vitorino, dan shekaru 61, wanda kuma na kusa ne da babban sakataren MDD, Antonio Guteres, ta zo ne bayan da 'yar takarar Costa Rica, Laura Thompson, wacce ita ce mataimakiyar shugaban hukumar ta OIM, ta janye takararta, bayan zagaye na hudu na zaben.

Tun kafa wannan hukuma a shekara 1951, Ba'amurke ne yake shugabancin hukumar mai mambobi 172, in ban da a shekara 1961 zuwa 1969 da wani dan Newzerland ya jagorance ta.

Wannan dai babbar nasara ce ga kasashen Turai, kuma hakan na zuwa ne bayan yarjejeniyar da suka cimma yau Juma'a kan yadda zasu tunkari matsalar kwararar bakin haure, musamman kan tsugunnar dasu tun ma kafin su sanya kafa a kasashen turan.