Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Gargadi Akan Gurbatar Yanayi
(last modified Thu, 21 Jun 2018 12:06:40 GMT )
Jun 21, 2018 12:06 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Gargadi Akan Gurbatar Yanayi

Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato majiyar MDD dangane da rahoton "Ci Gaba Mai Dorewa 2018" wanda ya ambaci gurbar yanayi da hatsarin da ke tattare da shi

Wani sashe na rahoton ya ce; 91% na mazauna birane a duk fadin duniya suna shakar gurbatacciyar iska.

Bugu da kari rahoton ya ce a tsakanin shekarun 2000 zuwa 2014 mazauna birane sun karu daga kam miliyan 807 zuwa 883. Kasar Amurka ce a gaba wajen gurbataccen yanayi.

A cikin wannan yanayi ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da ficewar kasar daga cikin yarjejeniyar Paris akan kare muhalli daga ci gaba da gurbata.

Kasashe masu karfin arziki na duniya sun yi tir da matsayar ta Amurka akan muhalli.