Pars Today
'Yan majalisar dokokin kasar Pakistan sun yi watsi da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na tura sojoji zuwa kasar Saudiyya suna masu cewa hakan ya saba wa kudurin da Majalisar ta fitar da ta bukaci gwamnatin ta ci gaba da zama 'yar ba ruwanmu dangane da yakin da Saudiyyan ta kaddamar kan kasar Yemen.
A daidai lokacin da dangantaka ke kara tsami tsakanin kasashen Afganistan da Pakistan, hukumomin Islamabad sun kara matsa kaimi wajen korar 'yan gudun hijira Afganistan.
Rahotanni daga Pakistan na cewa mutane a kalla biyar ne suka gamu da ajalinsu a wani harin kunar bakin wake a wani coci dake kudu maso yammacin kasar.
Minsitan shari'a na kasar Pakistan, Zahid Hamid, ya mika takardar murabus dinsa ga firayi ministan kasar Shahid Khaqan Abbasi.
Kotun da ke kula da yaki da cin hanci da rashawa a Pakistan, ta bayar da sammacin kame tsohon firayi ministan kasar, Nawaz Sharif, bisa badakalar cin hanci da rashawa.
Rahotanni daga Indonesia, na cewa mutane a kalla 47 ne suka gamu da ajalinsu a wata mummunar gobar da ta auku a wani kamfanin safara ababen wasan wuta a wajen Jakarta babban birnin kasar.
Kungiyar Taliban na ci gaba da zazzafa kai hare harenta kan sojojin kasar Afganistan, inda ta kai hare hare guda uku a cikin sa'o'i 48 da suka gabata.
Manyan hafsoshin sojojin Iran da Pakistan sun bukaci kasashen duniya da su dau matakan da suka dace kuma na hakika wajen kawo karshen kisan kiyashin da ake yi wa musulmin Rohingya na kasar Myammar.
Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani yayi kakkausar suka ga irin tsoma bakin da manyan kasashen duniya suke yi cikin harkokin cikin gidan kasashen yankin Gabas ta tsakiya yana mai cewa kasashen yankin ne kawai za su iya tabbatar da tsaronsa.
Majalisar dokoki a Pakistan ta zabi Shahid Khaqan Abbasi a matsayin sabon Firaminista bayan kotun kolin kasar ta tube Nawaz Sharif kan badakalar rashawa a makon jiya.