Pakistan : An Fitar Da Sammacin Kame Nawaz Sharif
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i25183-pakistan_an_fitar_da_sammacin_kame_nawaz_sharif
Kotun da ke kula da yaki da cin hanci da rashawa a Pakistan, ta bayar da sammacin kame tsohon firayi ministan kasar, Nawaz Sharif, bisa badakalar cin hanci da rashawa.
(last modified 2018-08-22T11:30:54+00:00 )
Oct 26, 2017 11:21 UTC
  • Pakistan : An Fitar Da Sammacin Kame Nawaz Sharif

Kotun da ke kula da yaki da cin hanci da rashawa a Pakistan, ta bayar da sammacin kame tsohon firayi ministan kasar, Nawaz Sharif, bisa badakalar cin hanci da rashawa.

Sammacin da aka bayar na neman Nawaz Sharif, wanda kotun kolin kasar ta tsige a watan Yuli bisa laufukan cin hanci da karbar rashawa biyu, a cewar lauyensa Zafir Khan.

Wannan dai babban kalubale ne ga jam'iyyar tsohon firayi ministan kasar a daidai lokacin da ya rage kasa da shekara guda a je zaben 'yan majalisar dokokin kasar.

Shi dai Nawaz Sharif wanda yanzu haka ya ke da zama a Saudiyya, ana zargin iyallansa da mallakar kaddarori na fitar hankali a birnin Landan.