Taliban Ta Kai Mummunan Hari A Wani Barikin Sojin Afganistan
(last modified Thu, 19 Oct 2017 18:07:36 GMT )
Oct 19, 2017 18:07 UTC
  • Taliban Ta Kai Mummunan Hari A Wani Barikin Sojin Afganistan

Kungiyar Taliban na ci gaba da zazzafa kai hare harenta kan sojojin kasar Afganistan, inda ta kai hare hare guda uku a cikin sa'o'i 48 da suka gabata.

Na baya bayan nan shi ne na yau Alhamis wanda ya yi ajalin sojojin Afganistan a kalla 50 a wata barikin soji dake kudancin kasar.

A cewar ministan tsaron kasar, Janar Dawlat Waziri, sama da sojoji 60 ke cikin barikin a lokacin da aka kai harin na yau, inda 43 suka rasa rayukansu, kana wasu tara suka jikkata a yayin da ba a ji duriyar wasu shida ba.

Harin kuma a cewarsa ya yi raga raga da barikin babu abunda ya yi saura.

An dai harin ne da wata mota shake da bama-bamai a harabar barikin sojin.

Saidai wani mazaunin yankin ya ce a kalla mutane 50 suka mutu kana wasu ashirin na daban suka jikkata.

Wasu majiyoyi na daban sun ce maharan sun samu hadin kan wasu ne daga cikin barikin, wanda hakan ya basu damar shiga barikin.

Sanarwar da ma'aikatar tsaron ta fitar ta ce an kashe goma daga cikin maharan a wani farmakin ramuwar gayya da aka kai a yammacin kasar.

Tuni kungiyar Taliban ta ce ita keda alhakin kai harin.