Pakistan : Harin Kunar Bakin Wake Ya kashe Mutum 5 A Coci
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i26427-pakistan_harin_kunar_bakin_wake_ya_kashe_mutum_5_a_coci
Rahotanni daga Pakistan na cewa mutane a kalla biyar ne suka gamu da ajalinsu a wani harin kunar bakin wake a wani coci dake kudu maso yammacin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:31:09+00:00 )
Dec 17, 2017 11:11 UTC
  • Pakistan : Harin Kunar Bakin Wake Ya kashe Mutum 5 A Coci

Rahotanni daga Pakistan na cewa mutane a kalla biyar ne suka gamu da ajalinsu a wani harin kunar bakin wake a wani coci dake kudu maso yammacin kasar.

Hukumomin a yankin na Balouchistan sun ce wasu 'yan kunar bakin wake biyu ne suka kai harin da safiyar yau Lahadi, a yayin da ya rage 'yan kwanaki kadan a gudanar da bukukuwan Kirsimeti.

Wani jami'in 'yan sanda yankin mai suna Abdul Razzaq Cheema, ya ce maharan sun kusa kai a cikin cocin a lokacin da al'ummar ke ibadarsu ta mako mako.

Har zuwa lokacin fasara labarain, babu wata kungiya da ta dau alhakin kai harin.