-
An Ayyana Sabon Firayi Ministan Rikon Kwarya A Pakistan
Jul 30, 2017 05:56Bayan umarnin da kotun kolin kasar Pakistan ta bayar na sauke Firayi ministan kasar Nawaz Sharif daga kan mukaminsa a ranar Juma'ar da ta gabata, bisa zarginsa da hannu a cikin wata badakala ta cin hanci da rashawa, Nawaz Sharif ya sanar da yin murabus da kansa a jiya Ajiya Asabar.
-
An Nada Firayi Ministan Rikon Kwarya A Kasar Pakistan
Jul 29, 2017 17:02Jam'iyyar Pakistan Muslim League-Nawaz (PML-N) mai mulki a kasar Pakistan ta zabi ministan man fetur da albarkatun kasa na kasar Shahid Khaqan Abbasi a matsayin firayi ministan rikon kwarya na kasar wanda zai maye gurbin hambararren firayi ministan kasar Nawaz Sharif.
-
Pakistan: Kotun Koli Ta Yi Umarni Da A Sauke Nawaz Sharif Daga Mukamin Firayi Minista
Jul 28, 2017 18:22Babbar kotun kolin kasar Pakistan ta bayar da umarni da a sauke Firayi ministan kasar Nawaz Sharif daga kan mukaminsa, saboda abin da kotun ta ce ta samu hannunsa a wata barna da dukiyar kasa da aka tafka.
-
Pakistan Ta Aike Da Jiragen Bada Horo Zuwa kasar Katar
Jul 20, 2017 12:39Ma'aikatar tsaron kasar Katar ta sanar da cewa Pakistan ta aike da jiragen sama samfurin Super Moshak na bada horo.
-
Iran Ta Aike Da Sakon Ta'aziyya Da Alhini Ga Gwamnatin Kasar Pakistan
Jun 25, 2017 12:23Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta aike da sakon ta'aziyya ga gwamnatin Pakistan da al'ummar kasar kan hasarar rayukan da suka yi sakamakon fashewar wata tankar man fetur a kasar.
-
Mutane 57 Suka Mutu A Harin Pakistan
Jun 24, 2017 15:21Hukumomi a Pakistan sun ce adadin mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren da wasu 'yan kunar bakin wake suka kai jiya a wata kasuwar yankin Parachinar ya kai 57.
-
Harin Ta'addanci Ya Lashe Rayukan Mutane Masu Yawa A Kasar Pakistan
Jun 23, 2017 12:21Wata mota da aka makare da bama-bamai ta tarwatse a kusa da ofishin babban jami'in rundunar 'yan sandan garin Quetta da ke kudu maso yammacin kasar Pakistan.
-
Pakistan Ta Sake Bude Iyakarta Da Afganistan
May 27, 2017 15:27Hukumomi a Pakistan sun sanar da sake bude iyakar kasar da Afganistan a dalilin watan Azumin Ramadana, makwanni kadan bayan arangamar data wakana tsakanin sojojin kasashen biyu.
-
Kasashen Rasha, Iran, Iraki Da Syria Sun Tattauna Kan Batutuwa Na Tsaro
May 25, 2017 06:52Shugabannin majalisun tsaro na kasashen Rasha, Iran, Iraki da Syria, sun gudanar da zaman tattaunawa kan ayyukan hadin gwaiwa a tsakaninsu a kan batutuwa na tsaro.
-
Harin IS Ya Hallaka Mutane 17 A Pakistan
May 12, 2017 14:38Rahotanni daga Pakistan na cewa a kalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu kana wasu sama da 30 na daban suka raunana a wani harin kunar bakin wake da kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta dauki alhakin kaiwa.