An Nada Firayi Ministan Rikon Kwarya A Kasar Pakistan
(last modified Sat, 29 Jul 2017 17:02:59 GMT )
Jul 29, 2017 17:02 UTC
  • An Nada Firayi Ministan Rikon Kwarya A Kasar Pakistan

Jam'iyyar Pakistan Muslim League-Nawaz (PML-N) mai mulki a kasar Pakistan ta zabi ministan man fetur da albarkatun kasa na kasar Shahid Khaqan Abbasi a matsayin firayi ministan rikon kwarya na kasar wanda zai maye gurbin hambararren firayi ministan kasar Nawaz Sharif.

Rahotanni daga kasar sun bayyana cewar tsohon firayi ministan Nawaz Sharif shi ne ya zabi Shahid Khaqan Abbasi, a matsayin wanda zai maye gurbin nasa a wani zama da jami'iyyar ta gudanar a yau din nan; har ila yau kuma shi ne zai tsaya dan takarar jam'iyyar a zaben da za a gudanar a shekara mai zuwa.

Shahid Khaqan Abbasi, dan shekaru 58 a duniya, wanda ya kasance daga cikin na kurkusa da tsohon firayi ministan Nawaz Sharif kuma mai masa biyayya zai rike wannan matsayi ne na tsawon kwanaki 45.

A jiya juma'a ce dai Nawaz Sharif yayi murabus daga mukaminsa bayan da Kotun Koli ta kasar ta sauke shi daga mukamin nasa  bayan wani bincike da aka yi kan dukiyar iyalinsa sakamakon abin kunyar nan na Panama Papers ya gano cewa yana da dukiya a kasashen da ke kaucewa biyan haraji. Har ila yau kotun ta ba da umurnin a gudanar da bincike kan Sharif, dan shekaru 67 da iyalansa kan wannan lamarin don gurfanar da su a gaban kotu.