An Ayyana Sabon Firayi Ministan Rikon Kwarya A Pakistan
Bayan umarnin da kotun kolin kasar Pakistan ta bayar na sauke Firayi ministan kasar Nawaz Sharif daga kan mukaminsa a ranar Juma'ar da ta gabata, bisa zarginsa da hannu a cikin wata badakala ta cin hanci da rashawa, Nawaz Sharif ya sanar da yin murabus da kansa a jiya Ajiya Asabar.
Nawaz Sharif ya yi murabus ne a zaman da jam'iyyarsa ta Muslim League Nawaz ta gudanar a jiya a Asabar a birnin Islam-abad, tun kafin majalisar dokokin kasar ta tsige shi, ya kuma bayyana dan uwansa Shahbaz Sharif a matsayin wanda zai gaje shi.
Kotun Koli ta kasar Pakistan ta sauke shi daga mukamin nasa ne bayan wani bincike da aka yi kan dukiyar iyalinsa, sakamakon bincike da aka fi sani da Panama Papers ya gano cewa Nawaz Sharif yana da dukiya a kasashen da ke kauce wa biyan haraji. Har ila yau kotun ta ba da umurnin a gudanar da bincike kan Sharif, dan shekaru 67 da iyalansa kan wannan lamarin domin gurfanar da su a gaban kuliya, duk kuwa da cewa Sharif ya musunta wannan zargi.
Sai dai kafin lokacin da majalisar dokokin Pakistan za ta zabi sabon Firayi ministan kasar, Nawaz Sharif ya ayyana Shahid Khaqan Abbasi dan shekaru 58 a matsayin wanda zai rike matsayin Firayi ministan Pakistan na wucin gadi.
Abbasi dai daya ne daga cikin na hannun damar Nawaz Sharif, wanda yake rike da mukamin ministan mai da albarkatun kasa a Pakistan tun daga lokacin da Sharif ya sake darewa kan kujerar firayi ministan kasar a karo na uku a cikin shekara ta 2013.
Ya yi karatu a kasashen Amurka da Saudiyya a bangaren injiniya na wutar lantarki, kafin daga bisani ya shiga harkar siyasa, bayanin kisan mahaifinsa wanda ya kasance ne a cikin gwamnatin Diya'ul Haq a cikin shekara ta 1988. Tun daga lokacin an zabi Abbasi har sau shida a matsayin dan majalisar dokokin kasar, amma a cikin shekara ta 1999 bayan juyin mulkin da Parviz Musharraf ya yi Nawaz Sharif, an kame Abbasi tare da tsare shi a gidan kaso har tsawon shekaru biyu, bisa zarginsa da hannu a yunkurin yi wa gwamnatin Parviz Musharraf juyin mulki.
A cikin shekara ta 2003, Abbasi ya kafa kamfanin safarar jiragen sama na Airblue, wanda a halin yanzu shi ne kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na biyu mafi karfi kasar ta Pakistan, bayan kamfanin kamfanin PIA mallakin gwamnatin kasar.
Duk da cewa dai wannan mataki ya yi wa jam'iyyun da ke adawa da gwamnatin Nawaz Sharif dadi matuka, amma kuma a lokaci guda hakan wata manuniya ce a kan cewa, an bude wani sabon shafi na wata sabuwar dambarwar siyasa a kasar, musamman ganin yadda magoya bayansa suka fara gudanar da zanga-zangar kin amincewa da hukuncin na kotu, yayin da magoya bayan jam'iyyun adawa da sauran bangarorin da ba su ga maciji da Nawaz Sharif, suke nuna goyon bayansu dari bisa dari a kan wannan hukunci na kotu, wanda ya kawo karshen mulkin Nawaz Sharif.