-
Qatar : Ba Za Mu Dauki Mataki Ba, Kan 'Yan Kasashen Da Suka Katse Huldar Da Mu
Jun 12, 2017 05:43Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Qatar ta ce kasar ba tada wani shiri na daukar wani mataki kan baki dake zaune a kasar wadanda kasashensu suka katse huldar jakadanci da ita ba, haka kuma ba za ta dauki matakai na rage matsayin huldar jakadanci da su ba.
-
Saudiyyah Ta Hana 'Yan Qatar Shiga Harami Domin Yin Umrah
Jun 11, 2017 21:39Sakamakon yanke alakar da Saudiyya tare da wasu kasashen da gwamnatin Qatar, mahukuntan saudiyya sun hana wasu 'yan kasar Qatar gudanar da aikin Umrah.
-
Qatar Ta Gode Wa Iran Saboda Kokarinta Na Magance Rikicin Da Ya Kunno Kai Tsakaninta Da Saudiyya
Jun 10, 2017 17:11Ministan harkokin wajen kasar Qatar Muhammad bn Abdurrahman Al Thani ya jinjinawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma gode mata saboda irin kokarin da take yi wajen magance rikicin da ya kunno kai tsakaninta da wasu kasashen larabawa karkashin jagorancin kasar Saudiyya.
-
Rarrabuwar Kawukan Kasashen Larabawa Kan Rikicin Qatar Da Saudiyya.
Jun 09, 2017 07:10Kasashen larabawa sun sami sabadi a tsakaninsu kan rikicin da ke faruwa tsakanin gwamnatocin kasashen Saudia da kuma kasar Qatar, wanda ya kai ga katse dangantakar jakadanci da kuma rufe kan iyakokin kasashen biyu ta sama da kasa.
-
Saudiyya, UAE, Bahrain, Masar, Suna Ci Gaba Da Kara Matsa Lamba A Kan Qatar
Jun 09, 2017 06:25Kasashen Saudiyya, UAE, Bahrain da Masar, sun fitar da wani bayani a jiya na hadin gwiwa, da ke saka wasu mutane 59 da kuma wasu cibiyoyi da kungiyoyi 12 da suka ce suna da alaka da Qatar a cikin jerin wadanda suke kira 'yan ta'adda.
-
Qatar Ta Ce Za Ta Iya Jurewa Duk Wani Irin Mataki
Jun 08, 2017 18:00Kasar Qatar ta ce za ta iya jurewa kan duk wani irin mataki da kasashe makoftanta zasu dauka akanta, aman ba zata taba mika kai ba.
-
Wasu Kasashen Afirka Sun Yanke Alakar Su Da Kasar Qatar
Jun 08, 2017 11:54Bayan da wasu kasashen Larabawa suka yanke alakar Diplomasiyar su da kasar Qatar, Wasu daga cikin kasashen Afirka ma sun kira Jakadunsu daga kasar
-
Rashin Damuwar Gwamnatin Kasar Masar Da dubban Daruruwan Misrawa A Qatar
Jun 07, 2017 14:17Matakin da gwamnatin kasar Masar ta dauka na katse dangantaka da kasar Qatar domin neman yardar Kasashen Saudiya da Emarate ya fusata misrawa kimani dubu 250 da ke zaune a kasar Qatar
-
Takun-Saka Tsakanin Qatar Da Saudiyya Na Kara Tsananta
Jun 07, 2017 08:05Tun bayan da rikicin da ke tsakanin Saudiyyah da Qatar ya fito fili sakamakon sanar da yanke dukkanin alaka da kasar Saudiyya ta yi da Qatar kwanaki uku da suka gabata, lamurran suna ci gaba da kara dagulewa a tsakanin kasashen larabawan yankin tekun Fasha.
-
Trump Ya Ce Larabawa Sun Sanar Da Shi Qatar Tana Goyon Bayan 'Yan Ta'adda
Jun 06, 2017 18:09Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewar shugabannin Saudiyya da kawayenta sun bayyana masa cewar kasar Qatar tana taimakawa masu tsaurin ra'ayi na ta'addanci da kudade bayan da ya bukace su da kawo karshen taimakon kungiyoyin ta'addanci.