Qatar Ta Ce Za Ta Iya Jurewa Duk Wani Irin Mataki
Kasar Qatar ta ce za ta iya jurewa kan duk wani irin mataki da kasashe makoftanta zasu dauka akanta, aman ba zata taba mika kai ba.
Ministan harkokin wajen kasar ta Qatar ne, cheikh Mohammed ben Abderrahmane Al-Thani, ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dilancin labaren AFP, a daidai lokacin da takaddamar diflomatsiya ke kara tsami tsakanin kasarsa da makoftanta.
A ranar Litinin data gabata ce Saudiya da kawayenta suka katse duk wata irin hulda da kasar ta Qatar bisa zarginta da goyan bayan ayyukan ta'addanci, zargin da kasar ta Qatar ke ci gaba da musuntawa.
A hannu daya kuma kasar ta Qatar ta yi watsi da jitan-jitan dauka matakin soji a iyakokinta da Saudiyya akan wannan takaddama.
Mista Al-Thani ya kara da cewa babu wani mahaluki da yake da hurimin shiga harkokin da suka shafi manufofin kasar na ketare.
Su dai Kasashen na son kasar Qatar ta canza siyasarta, kana kuma suna bukatar gidan talabijinna Al-Jazeera mallakar Qatar din da ya daina tsauraran farfaganda, sannan kuma mahukunta Doha sun dauki mataki kan kungiyar 'yan uwa musulmi da kuma wasu kungoyoyin kishin islama dake da mazauni a Doha.