Wasu Kasashen Afirka Sun Yanke Alakar Su Da Kasar Qatar
(last modified Thu, 08 Jun 2017 11:54:48 GMT )
Jun 08, 2017 11:54 UTC
  • Wasu Kasashen Afirka Sun Yanke Alakar Su Da Kasar Qatar

Bayan da wasu kasashen Larabawa suka yanke alakar Diplomasiyar su da kasar Qatar, Wasu daga cikin kasashen Afirka ma sun kira Jakadunsu daga kasar

Bayan da Kasashen Saudiya, Hadaddiyar daular Larabawa, Bahrein, Masar da Libiya suka yanke alakar Diplomasiyar su da kasar Qatar, a jiya Laraba, wasu kasashen Afirka da suka hada da Senegal, Djibouti, Gabon, Sudan da Somaliya sun yi alawadai da goyon bayan 'yan ta'adda da kasar Qatar din ke yi.

Kasar Senegal ta kira Jakadanta daga birnin Doha kafin a samu mafitar siyasa tsakanin kasashe 5 na Larabawan da kasar Qatar, ita kuma kasar Djibouti, domin kare mutuncinta ta ce za ta rage jami'an Diplomasiyar ta a birnin Doha.

A nata Bangare kasar Gabon ta yi alawadai da goyon bayan 'yan ta'adda da kasar Qatar din ke yi,inda ta kira ta da ta mutunta dokar kasa da kasa wajen yaki da ta'addanci, su kuma kasashen Sudan da Somaliya sun bayyana damuwar su kan matakin da kasashen biyar na Larabawa suka dauka dangane da kasar ta Qatar, inda suka kira su da su zauna kan tebirin tattaunawa domin magance matsalar.