Rashin Damuwar Gwamnatin Kasar Masar Da dubban Daruruwan Misrawa A Qatar
Matakin da gwamnatin kasar Masar ta dauka na katse dangantaka da kasar Qatar domin neman yardar Kasashen Saudiya da Emarate ya fusata misrawa kimani dubu 250 da ke zaune a kasar Qatar
Kamfanin dillancin Labaran SkyNews ya nakalto cewa akwai akalla misrawa dubu 250 a kasar Qatar wadanda katse dangantakan da gwamnatin kasar Masar ta yi da kasar Qatar ya jefa cikin tashin hankali. Wannan matakin dai ya sanya wadan nan Misrawa cikin fargaba idan har gwamnatin Qatar ta bukaci su da su bar kasarta.
A lokacinda aka tambayi shugaban kasar ta Masar kan abinda zai biyo bayan matakin da ta dauka kan kasar Qatar da kuma yadda abin zai shafi yan kasar da suke can, sai ya ce su dawo gida don akwai wuraren aikin isassu, wannan amsar dai ta fusata misrawa da dama, don sanin irin halin da kasarsu take ciki na tashin aikin yi da kuma matsalolin tattalin arziki.