Rarrabuwar Kawukan Kasashen Larabawa Kan Rikicin Qatar Da Saudiyya.
Kasashen larabawa sun sami sabadi a tsakaninsu kan rikicin da ke faruwa tsakanin gwamnatocin kasashen Saudia da kuma kasar Qatar, wanda ya kai ga katse dangantakar jakadanci da kuma rufe kan iyakokin kasashen biyu ta sama da kasa.
Wannan rikicin dai ya kara bayyana irin barakan da ke tsakanin wadannan kasashe a fili.
Kasashen larabawan wadanda yawansu ya kai 22 dai sun saba a tsakannsu a wajen nuna goyon baya ko kuma yin watsi da matakin da kasar ta Saudia ta dauka a kan kasar Qatar, bayan zarginta da goyon bayan ayyukan ta'addanci da kuma kusantar kasar Iran inda wasu daga cikinsu suka goyi bayan kasar ta Saudia, suka kuma katse huldan jakadancin da kuma ta zirga zirgan jiragen sama ta sama da ta ruwa tsakaninsu da kasar Qatar don neman yadar kasar Saudia.
Kasashen da suka dauki wannan matakin dai sun hada da Emirate, Bahrain, Masar, Libya da kuma Mauritania. Sai kuma kasashen Sudan da Somalia wadansa suka bukaci kasashen biyu su sasanta a tsakaninsu ba tare da sun taba dangantakarsu da Qatar ba.
Sannan banda haka akwai wasu kasashen Afrika wadanda basa cikin kungiyar kasashen ta Larabawa amma kuma suka katse dangantakarsu da kasar Qatar don neman yardar kasar saudia, wadannan kasashe sun hada da Senegal da Gabon.
A dayan bangaren kuma wasu kasashen kungiyar ta Larabwa sun raje huldansu da kasar Qatar ne kawai, don nuna goyon bayansu da gakar da Saudia sun kuma hada da Kuwait, Morocco, Jordan da Kommoros.
Sai kuma bangare na ukku wadanda basu ma tankawa kasar ta Saudia a kan Lamarin gaba daya, sun bar dangantarsu da Qatar kamar yadda take wadannan kasashe sun hada da Iraqi, Syria, Algeria, Tunisia, Kuwait da kuma Lebanon.
Sai dai wani abin lura a nan shi ne cewa wasu kananan kasashen, masu neman yadar kasar saudia a wannan matakin basu da wani tasiri ko muhimmancin a cikin kungiyar sai dai sun biye kasar Saudia ce don kawai watakila kada su rasa abinda suke samu a wajenta. Irin wadan nan kasashe sun hada da Mauritania, Komorus , Njubuti da Somalia.
Amma kasar Sudan muna iya cewa ta duba lamarin daga bangarori biyu kafin ta dauki matsayi, don kamar yadda take bukatar taimakon kasar Saudia haka take buktar na kasar Qatar. Kowa ya san cewa kasar Qatar ta zuba jari mai yawa a kasar Sudan. Ban haka sau da dama tana daukar nauyin shiga tsakani don sasantawa tsakanin gwamnatin Sudan da yan tawaye kasar, don warware wasu matsalolin cikin gida na kasar Sudan.
Daga karshe dai masana suna ganin bijirewar kasashen Larabawa musamman kanana daga cikinsu ga kasar Saudia, ya nuna cewa da dama daga cikin kasashen sun dawo daga rakiyarta a matsayin wacce take fada a ji a cikin kungiyar mai kasashen 22, kuma wannan zai sauyin tabbas zai shafi kasashen a bangarori daban daban nan gaba.