Pars Today
Kasashen Amurka da Rasha na ci gaba da samun sabani kan rikicin kasar Venezuela, inda kasashen biyu suka gabatar da kudurorin doka mabambanta kan kasar a zauren kwamitin tsaro na MDD.
Kakakin shugaban kasar Rasha ya ce kokarin da kasashen Yamma ke yi na amincewa da Juan Guaido madugun 'yan adawan kasar Venezula a matsayin shugaban kasa, katsa landan ne ga al'amuran cikin gidan kasar
Shugaba Vladimir Putin, na Rasha, ya sanar a yau Asabar da janye kasarsa daga yarjejeniyar takaita kera makamman nukiliya ta INF dake tsakanin Rashar da Amurka.
Majiyar shari'a a kasar Rasha ta bada sanarwan cewa an yanke hukunci na zaman kaso mai tsawo ga wasu yayan kungiyan yan ta'adda ta Daesh su biyar.
Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya bada sanarwan ficewar kasar Amurka daga yerjejeniyar hana kirar makamai masu linzamin masu kaiwa matsakaicin zanga tsakaninta na Rasha.
Kasashen China da Rasha sunyi allawadai da sabbin takunkuman da Amurka ta kakaba wa kasar Venezuela.
Gwamnatin kasar Rasha ta bada sanarwan cewa za'a gudanar da taro dangane da matsalar al-ummar Palasdinu a ranakun 13 da 14 na watan Febreru mai kamawa a birnin Moscow.
Gwamnatin kasar Amurka, a ci gaba da shirinta na gurgunta gwamnatin JMI zata gudanar da taro ta musamman a birnin Waso na kasar Poaland daga ranar 13 zuwa 14 na watan Febreru mai kamawa.
Kasar Rasha ta ce, Amurka ce silan dakatar da yarjejeniyar kayyade makaman nukiliya wadanda ke iya kaiwa ko wacce kasa dake tsakanin kasashen biyu.
Sojojin Rasha sun fara sintirin ne dai a daidai lokacin da kasar Turkiya take barazanar shiga cikin yankin Manbaj domin yakar rundunar kurdawa