Rasha Zata Dauki Bakuncin Taro Kan Palasdinu
(last modified Sat, 26 Jan 2019 11:59:47 GMT )
Jan 26, 2019 11:59 UTC
  • Rasha Zata Dauki Bakuncin Taro Kan Palasdinu

Gwamnatin kasar Rasha ta bada sanarwan cewa za'a gudanar da taro dangane da matsalar al-ummar Palasdinu a ranakun 13 da 14 na watan Febreru mai kamawa a birnin Moscow.

Tashar talabijin ta Almayadee ta kasar Lebanon ta nakalto majiyar gwamnatin kasar Rasha na fadar haka a jiya Jumma'a . Ta kuma kara da cewa dukkan kungiyoyin Palasdinawa, wadanda suka hada da Hamas da Jahadul Islami duk zasu sami damar halattan taron.

Rasha ta kara da cewa ta shirya wannan taron ne dai-dai da taron da Amurka ta shirya za'a gudanar a birnin Waso na kasar Holand don a taron na Waso ba'a kawo batun Palasdinawa ba, duk da cewa batun ne ya fi muhimmanci a yankin gabas ta tsakiya.

A taron Waso dai sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya bayyana cewa zasu tattauna batun yankin gabas ta tsakiya, makamai masu linzami na kasar Iran da kuma irin tasirin da Iran take yi a yankin.