Rasha : Amurka Ce Silan Soke Yarjejeniyar Kayyade Makamman Nukiliya
(last modified Tue, 15 Jan 2019 18:22:20 GMT )
Jan 15, 2019 18:22 UTC
  • Rasha : Amurka Ce Silan Soke Yarjejeniyar Kayyade Makamman Nukiliya

Kasar Rasha ta ce, Amurka ce silan dakatar da yarjejeniyar kayyade makaman nukiliya wadanda ke iya kaiwa ko wacce kasa dake tsakanin kasashen biyu.

Wannan bayanin ya fito ta bakin karamin ministan harkokin wajen Rashar, Sergio Riabkov, bayan tattaunawar da kasashen biyu suka gudanar a birnin Geneva.

Mista Riabkov, ya ce duk abunda ya biyo baya laifin Amurka ce, don bayan tattaunawar mun fahimci cewa, Amurka ta darma niyyar ficewa data yarjejeniyar ce.

Bayanai sun nuna cewa an watse a tattaunawa ba tare da cimma wata mastaya ba tsakanin bangarorin biyu.

Jami'in Rashar ya kara cewa babu wata matsaya da aka cimma yayin tattaunawar, kuma kawo yanzu babu wata rana da aka tsaida domin wata tattaunawar, amma ya ce a shirye kasarsa take don ci gaba da tattaunawa saidai a ckin mutunci da girmamawa ba tare da barazana ba.

Amurka da kungiyar tsaro ta NATO na zargin mahukuntan Rasha da sabawa yarjejeniyar da suka cimma ta kayyade makamman nukiliya da suke kerawa da kasashen biyu suka cimma a shekarar 1987.

Amurka ta ce Rasha ta sabawa yarjejeniyar ce ta hanyar kera wasu sabbin makamai masu linzami, zargin da Rashar ta musanta tana mai cewa marar tushe ne, tare ita ma da zargin Amurka da sabawa yarjejeniyar.

A tsakiyar watan Disamba da ya gabata, shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya bayyana wani sabon shirin kasarsa na kera wasu sabbin makamai masu linzami, da yarjejeniyar da suka cimma ta haramta middin Amurka ta janye daga yarjejeniyar.