Pars Today
An yi taho mu gama din ne a garin Beithlehem da ke yammacin kogin Jordan, tare da kame matasan Palasdinawa 16 da 'yan sahayoniya.
Labaran da suke fitowa daga garin misrata na kasar Libya sun nuna cewa ana kai fafatawa tsakanin bangarori biyu a tsowan daren jiya Lahadi.
Sakamakon barkewar wani sabon rikici a garin Jos, babban birnin jihar Filato a Nijeriya, gwamnan jihar Filato din Simon Lalong ya sanar da sanya dokar ta baci ta sai baba ta gani a garin.
Gwamnatin Jahar Abia ta sanar da kafa dokar ta bacin ne ta kwanaki biyu wacce za ta fara daga gobe alhamis.
Dauki ba dadi ya kunno kai tsakanin jami'an tsaron Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da gungun 'yan adawar kasar a birnin Kinshasa fadar mulkin kasar ta Dimokaradiyyar Congo a jiya Lahadi.
Gumurzu ya kunno kai tsakanin sojojin gwamnatin Libiya da gungun 'yan ta'addan kungiyar Da'ish a yankin Al-Wadi Humur da ke shiyar gabashin garin Sirt na kasar.
Jami'an tsaro sun yi awon gaba da mutane 11 daga cikin 'yan adawar kasar, biyo bayan gudanar da wani gangami da gwamnatin kasar ta haramta, wanda aka gudanar domin nuna goyon baya ga madugun adawa na kasar Jan Ping.
Cibiyar watsa labarun kasar Libya ta Libyan Express ya nakalto jami'an kasar ta Libya suna cewa; An kashe mutane 9 a fadan da aka yi akan iyaka da Chadi.
Akalla mutane 50 ne suka rasa rayukansu sakamakon barkewar wani rikcin kabilanci a jamhuriyar Dimkradiyyar Congo, tare da jikkatar wasu da dama.
Wani sabon rikicin kabilanci da ya barke a yankin Darfur da ke yammacin Sudan, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 tare da jikkatar wasu.