Congo: Mutane 50 Sun Rasa Rayukansu A Wani Rikicin Kabilanci
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22956-congo_mutane_50_sun_rasa_rayukansu_a_wani_rikicin_kabilanci
Akalla mutane 50 ne suka rasa rayukansu sakamakon barkewar wani rikcin kabilanci a jamhuriyar Dimkradiyyar Congo, tare da jikkatar wasu da dama.
(last modified 2018-08-22T11:30:30+00:00 )
Aug 07, 2017 06:42 UTC
  • Congo: Mutane 50 Sun Rasa Rayukansu A Wani Rikicin Kabilanci

Akalla mutane 50 ne suka rasa rayukansu sakamakon barkewar wani rikcin kabilanci a jamhuriyar Dimkradiyyar Congo, tare da jikkatar wasu da dama.

A wata zantawa da manema labarai da ya yi a yammacin jiya, shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula na yankin Tanganyika a jamhuriyar dimukradiyyar Congo Tambana Nbami ya bayyana cewa, rikicin ya barke ne a tsakanin kabilun  Pygmées Twa da kuma Bantous Lubas, inda mutane akalla 50 suka rasa rayukansu daga bangarorin biyu.

Rikici tsakanin wadannan mayan kabilu biyu ya fara ne tun a cikin watan Agustan shekara ta 2016 da ta gabata, an tura tawagar masu shiga tsakani a jiya domin tattaunawa da shugabannin kabilun biyu, da nufin samo hanyoyin sulhu da kuma kawo karshen zaman doya da manja da kabilun biyu suke yi a yankin.