Dauki Ba Dadi A Garin Misrata A Kasar Libya
(last modified Mon, 18 Sep 2017 06:26:40 GMT )
Sep 18, 2017 06:26 UTC
  • Dauki Ba Dadi A Garin Misrata A Kasar Libya

Labaran da suke fitowa daga garin misrata na kasar Libya sun nuna cewa ana kai fafatawa tsakanin bangarori biyu a tsowan daren jiya Lahadi.

Shafin yanar gizo na «بوابه افریقیا الاخباریه» ya nakalto majiyar jami'an tsaron kasar ta Libya tana cewa ana nan ana ta fafatwa tsakanin wata kungiya mai suna Anas- Addabbashi da kuma rundunar jami'an tsaron kasar mai yaki da ayyukan ta'addanci. 

Ya zuwa lokacin bada wannan labari dai mutum guda ya rasa ransa a yayin da wasu 7 kuma suka ji rauni. Wata majiyar ta kara da cewa kungiyar Anas Addabbashi kungiya ce ta yan ta'adda wacce take biyayya ga kungiyar Daesh. 

Tun shekara ta 2011 ne lasar Libya ta fada cikin tashe-tashen hankula bayan faduwar gwamnatin Mo'amma Kazzafi. A halin yanzu kasar tana da gwamnatoci biyu ne, daya mai cibiya a babban birnin kasar Tripoli karkashin jagorancin Priministan hadin kan kasa Fa'iz Suraj da kuma Gwamnatin Gabacin kasar wacce babban kwamandan sojojin kasar Halifa haftar yake jagoranta.

Majlisar dokokin kasar dai wacce take da mazauni na Tabrag tana goyon bayan Khalifa Haftar ne.