Sudan: Rikicin Kabilanci A Darfur Ya Lashe Rayukan Mutane 10
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22536-sudan_rikicin_kabilanci_a_darfur_ya_lashe_rayukan_mutane_10
Wani sabon rikicin kabilanci da ya barke a yankin Darfur da ke yammacin Sudan, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 tare da jikkatar wasu.
(last modified 2018-08-22T11:30:26+00:00 )
Jul 24, 2017 16:43 UTC
  • Sudan: Rikicin Kabilanci A Darfur Ya Lashe Rayukan Mutane 10

Wani sabon rikicin kabilanci da ya barke a yankin Darfur da ke yammacin Sudan, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 tare da jikkatar wasu.

Rahotanni daga kasar Sudan sun tabbatar da cewa, rikicin ya barke ne a tsakanin kabilun Raqib masu alaka da larabawa, da kuma Ruzaikat bakaken fata, kuma rikicin ya faru ne a garin Da'in da ke cikin lardin Darfur.

A cikin watan Afirilun da ya gabata ma wani rikici makamancin wannan ya barke a yankin, wanda shi ma ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 9.

Wasu daga cikin kabilun bakaken fata a yankin darfur suna zargin gwamnatin Sudan da mara baya ga kabilun da suke da alaka da larabawa, domin muzgunawa kabilun bakaken fata.