Pars Today
A jiya Lahadi da yamma ce aka kawo karshen kace-nace tsakanin kasashen turai dangane da jirgin ruwa dauke da bakin haure fiye da 600 bayan da kasar Italia ta ki karbansu.
Kasar Rasha, ta ce ba ta da wata niyyar komawa cikin kungiyar kasashe mafiya tattalin arzikin a duniya na G7, a halin yanzu.
Kasashen mafiya karfin tattalin arziki na duniya da ake kira G7, sun kammala taronsu a jiya Asabar, tare da nuna adawa da sabuwar siyarar kasuwancin Amurka.
Babbar jami'ar kula da harkokin kasashen ketare na kungiyar tarayya turai, Federica Mogherini ta bayyana cewa, batun nukiliyar Iran na shafar tsaron kungiyar, maimakon tattalin arziki.
Rahotanni daga Belgium na cewa, wani dan bindiga ya hallaka mutum uku, da suka hada da 'yan sanda biyu a birnin Liège dake gabashin kasar.
Wakiliyar Cibiyar tsaro da taimakekkeniya ta musamman a fagen yaki da fataucin mutane a kasashen yammacin Turai ta yi furuci da cewa: Akwai mutane fiye da miliyan ashirin da biyar a fadin duniya da ake bautar da su.
Mafi yawan kasashen yammacin turai sun ki karba goron gayyata domin halartar bikin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Quds mai alfarma.
Shugabannin kasashen Iran da Faransa sun tattauna ta wayar tarho kan muhimman batutuwa da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma batun yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya.
An fara atisayen sojin hadin gwiwa na dakarun kasashe ashirin daga nahiyar Afirka, da na yammacin duniya a karkashin jagorancin Amurka da ake kira ''Flintlock.
Mahukumtan kungiyar tarayyar Turai na neman kimanin masu safarar bakin haure zuwa nahiyar su dubu 65, adadin da ya rubanya sau biyu a cikin shekaru 3 da matsalar kwararar bakin hauren ta ta’azara a nahiyar.