Turai Na Farautar Masu Safarar Bakin Haure Dubu 35
Mahukumtan kungiyar tarayyar Turai na neman kimanin masu safarar bakin haure zuwa nahiyar su dubu 65, adadin da ya rubanya sau biyu a cikin shekaru 3 da matsalar kwararar bakin hauren ta ta’azara a nahiyar.
Cikin wata sanarwar da hukumar yaki da masu fasa kwabrin bakin haure ta turai ta fitar ta ce duk da nasarar da aka samu na raguwar yawan bakin hauren dake yi nasarar kutsa kai a nahiyar turai ta hanyar tekun Medetaraniyan a 2016, har yanzu matsalar na nan daram,
A binciken da mahukumtan kasashen turan suka bada umarnin gabatarwa, ya nuna cewa, yanzu haka sannu a hanakli ana ci gaba da tantance masu aikata wannan laifi
Robert Crepinko, shugaban sashen dake kula da shige da ficen baki na nahiyar turai ya sanar da AFP cewa, a karshen shekarar da ta gabata suna da sunayen kimanin masu safarar bakin hauren zuwa turai dubu 65 akan girgam
A shekara ta 2015 yawan masu wannan aiki na laifi su dubu 30 ne, kafin su zama dubu 55 a 2016, a yayin da a shekarar 2017 da ta gabata yawansu ya karu da dubu 10 inda ajimilce suka kai dubu 65.