Dan Bindiga Ya Hallaka Mutum 3 A Belgium
https://parstoday.ir/ha/news/world-i31232-dan_bindiga_ya_hallaka_mutum_3_a_belgium
Rahotanni daga Belgium na cewa, wani dan bindiga ya hallaka mutum uku, da suka hada da 'yan sanda biyu a birnin Liège dake gabashin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:31:54+00:00 )
May 29, 2018 11:19 UTC
  • Dan Bindiga Ya Hallaka Mutum 3 A Belgium

Rahotanni daga Belgium na cewa, wani dan bindiga ya hallaka mutum uku, da suka hada da 'yan sanda biyu a birnin Liège dake gabashin kasar.

Bayanai daga kasar dai sun ce jami'an tsaro sun bindige maharin bayan da ya yi garkuwa da wani mutum, a lokacin da ya shiga wata makarantar sakandare.

Tuni dai aka fara danganta lamarin da na ta'addanci.

Kasar Belgium dai ta taba fuskantar harin maykan dake ikirari da sunan jihadi, a watan Maris na shekara 2016, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 32.