An Fara Atisayen Sojin Amurka Dana Kasashen Yamma A Afrika
An fara atisayen sojin hadin gwiwa na dakarun kasashe ashirin daga nahiyar Afirka, da na yammacin duniya a karkashin jagorancin Amurka da ake kira ''Flintlock.
An fara atisayen ne a jiya Litini a yankin Agades da ke arewacin jamhuriyar Nijar inda kusan dakaru 1,900 zasu kwashe kwanaki 11 suna atisayen.
kamar yadda wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta fitar
Sanarwar ta ce za a gudanar da atisayen na bana ne a wurare daban-daban baya ga Nijar, wadanda suka hada da Burkina Faso da Senegal daga ranar 9 zuwa 20 ga watan nan na Afrilu.
Atisayen na bana na da manufar kara karfafa karfin aikin sojan kasashen yankin wajen yaki da kungiyoyin masu tsatsauran ra'ayi, a cewar rundunar sojin Amurka dake aiki a nahiyar Afrika (Africom).
Dakarun da za su shiga cikin atisayen sun hada da na kasashen Burkina Faso da Kamaru da Chadi da Mali da Mauritania da Nijar da Najeriya da Senegal da kuma wasu kasashe 12 na yammacin duniya.