Taron Kasashen G7 Ya Sake Maida Amurka Saniyar Ware
(last modified Sun, 03 Jun 2018 05:51:09 GMT )
Jun 03, 2018 05:51 UTC
  • Taron Kasashen G7 Ya Sake Maida Amurka Saniyar Ware

Kasashen mafiya karfin tattalin arziki na duniya da ake kira G7, sun kammala taronsu a jiya Asabar, tare da nuna adawa da sabuwar siyarar kasuwancin Amurka.

Kasashen kawayen Amurka sun zasu hadu wani taro a birnin Quebec domin bukatar mahukuntan na Washigton dasu sake nazari kan matakin na biyan harajin karafa.

Ministocin kudi da gwamnonin bankin kasashen sun bukaci sakataren kudi na Amurka, Steven Mnuchin, da ya mika matukar damuwarsu da kuma takaicinsu ga gwamnatin ta Amurka kan sabon tsarin na kakaba wa Turai da Canada da Mexico haraji.

Kasashen sun cimma matsaya guda ta tattaunawa don daukar mataki kan matakin na Amurka.

Ministan kudin Faransa Bruno Le Maire ya bayyana a wajen taron na kungiyar ta G7 da aka yi a Canada cewa, Amurka na da yan kwanaki kadan domin sauya matsayin da ta dauka kan kasashen ko kuma ta gamu da fushinsu.