Pars Today
Ma'aikatar harakokin wajen jamhoriyar musulinci ta Iran ta yi Allah wadai kan ta'addancin da kawancen Saudiya ya kaiwa motar Bas din dake dauke da yara 'yan makaranta a lardin Dahyan na jahar Sa'ada da ya yi sanadin mutuwar 39 da kuma jikkatar wasu 51 na daban.
Sojojin mamayar masarautar Saudiyya biyar sun halaka a yankin kudancin kasar Yamen kusa da kan iyaka da kasar Saudiyya.
Wani harin sama da kawancen da Saudiyya ke jagoranta a yakin Yemen, ya yi sanadiin mutuwar yara 'yan makaranta a kalla 39 tare da jikkata wasu mutane 48 na daban a arewacin kasar ta Yemen.
Ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da jiragen yakin kawancen Saudiya ke kaiwa jihar Hudaida na kasar Yemen, Majalisar Dinkin Duniya ta ce lamarin ya jefa rayukan duban Mata masu juna biyu a yankin cikin hadari.
Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun kai wasu jerin hare-haren wuce gona da iri kan lardunan Sa'adah da Hudaidah da suke kasar Yamen.
Kakakin sojojin Kasar Yemen ya sanar da cewa; Sun kai hari da jirgi maras matuki akan cibiyar jiragen sama ta sarki Khalid da ke gundumar Asir a kudancin Saudiyya
Hukumar Kula da Kiwon Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya "WHO" ta yi gargadi kan yiyuwar bullar cutar kwalara a kasar Yamen.
Gwamnatin kasar Iran ta yi allawadai da kisan kiyashin da jiragen yakin saudia da kawayenta suke ci gaba da yi a kasar Yemen.
Wakilin Kasar Rasha a MDD ya ce ci gaban da daukan matakin soja ba zai taimaka wajen magance rikicin kasar Yemen ba.
Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun yi luguden wuta a lardin Sa'adah da ke arewacin kasar Yamen, inda suka kashe mutane biyu ciki har da karamin yaro guda.