Rasha : Matakin Soja Ba Zai Magance Rikicin Yemen Ba
Wakilin Kasar Rasha a MDD ya ce ci gaban da daukan matakin soja ba zai taimaka wajen magance rikicin kasar Yemen ba.
Tashar talabijin din Aljazera ta nakalto Vasily Nebenzya wakilin kasar Rasha a MDD jiya alhamis yayin zaman taron kwamitin tsaron MDD kan rikicin kasar yemen na cewa ta hanyar siyasa ce kawai za a iya magance rikicin kasar Yemen, kuma kowa ya san cewa ci gaba da daukan matakin soja ba zai taimaka wajen magance rikicin kasar yemen din ba.
Vasily Nebenzya ya ce Rasha na maraba da kirar da manzon musaman na MDD kan kasar yemen ya yi na gudanar da tattauna tsakanin bangarorin dake fada a yemen.
A daren jiya alhamis ne Manzon musaman na MDD kan kasar Yemen Martin Griffiths ya bayyana cewa a ranar 6 ga watan Dicembar, birnin Ganeva zai karbi bakuncin tattaunawar lalubo hanyar magance matsalar kasar Yemen a tsakanin bangarorin dake fada da juna.
Mista Vasily ya kara da cewa wajibi ne a tattabar da tsaro a bakin ruwan Alhudaida saboda mahimancin da yake da shi wajen isar da kai agaji a kasar ta Yemen.