Sojojin Mamayar Saudiyya Biyar Sun Halaka A Yankin Kudancin Kasar Yamen
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32708-sojojin_mamayar_saudiyya_biyar_sun_halaka_a_yankin_kudancin_kasar_yamen
Sojojin mamayar masarautar Saudiyya biyar sun halaka a yankin kudancin kasar Yamen kusa da kan iyaka da kasar Saudiyya.
(last modified 2018-08-22T11:32:13+00:00 )
Aug 10, 2018 12:20 UTC
  • Sojojin Mamayar Saudiyya Biyar Sun Halaka A Yankin Kudancin Kasar Yamen

Sojojin mamayar masarautar Saudiyya biyar sun halaka a yankin kudancin kasar Yamen kusa da kan iyaka da kasar Saudiyya.

Majiyar watsa labaran Saudiyya ta tabbatar da halakar sojojin kasarta guda biyar a yankin kudancin kasar Yamen kusa da kan iyaka da Saudiyya a dauki ba dadin da aka tsakaninsu da sojojin Yamen a yau Juma'a.

Har ila yau sojojin Yamen da dakarun sa-kai na kasar sun harba makamai masu linzami kan sansanin sojin Saudiyya da ke yankin Ummur-Rish a lardin Ma'arif na kasar Yamen lamarin da ya yi sanadiyyar tarwatsa sansani tare da halaka sojoji masu yawa.