Aug 09, 2018 11:53 UTC
  • MDD Ta Yi Gargadi Kan Halin Da Mata Masu Juna Biyu Ke Ciki A Hudaida na Kasar Yemen

Ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da jiragen yakin kawancen Saudiya ke kaiwa jihar Hudaida na kasar Yemen, Majalisar Dinkin Duniya ta ce lamarin ya jefa rayukan duban Mata masu juna biyu a yankin cikin hadari.

Kamfanin dillancin labaran Meher ya nakalto Asusun Kidayar Jama'a na Majalisar Dinkin Duniya UNFPA na ishara kan ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da kawancen Saudiya ke ci gaba da kaiwa a yamen na cewa ci gaba da rikici a jahar Hudaida  ya jefa mata masu juna biyu cikin hadari, musaman ma wadanda za su haifu a watan gobe.

Bayanin na Asusun Kidayar Jama'a na Majalisar Dinkin Duniya UNFPA ya ce kimanin mata masu juna biyu dubu 90 ke cikin wannan hadari kuma idan ba a ci gaba da ba su taimako ba to suna iya rasa rayukansu.

Rahoton ya ce yadda rikici yayi kamari a jahar Hudaida na Yemen ya takaita taimakon da ake bawa Mata masu juna biyu, kuma a halin da ake ciki akwai kimanin dubu 14 da suke bukatar kulawa ta musaman.

Tags