-
Laberia : Tsohon Ministan Taylor, Zai Gurfana Gaban Kotun Amurka
Jun 11, 2018 01:51A wani lokaci a yau Litinin, ake sa ran gurfanar da tsohon ministan tsaron, tsohon shugaban kasar Laberia, Charles Taylor, a birnin Philadelphie na Amurka.
-
Najeriya : Buhari Na Ziyara A Marocco
Jun 11, 2018 01:50Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya fara wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kasar Morocco, bisa goron gayyatar da sarki Mohammed VI ya yi masa.
-
MDD : Tamowa Na Kamari A Kewayen Tafkin Chadi
Jun 11, 2018 01:50Majalisar Dinkin Duniya, ta yi gargadi game da yadda matsalar karancin abinci mai gina jiki ke dada kamari a kewayen tafkin Chadi.
-
Jami'an Tsaron Libya Sun Tare Kwalekwalen Yan Gudun Hijira Biyu A Gabar Tekun Kasar
Jun 10, 2018 14:50Majiyar Jami'an tsaro na ruwa a kasar Libya ta bada sanarwan kama kwalekwale guda biyu dauke da bakin haure kimani 150 a gaban tekun kasar.
-
Gwamnatin Kasar Congo Ta Haramtawa Yan Kasar Mazauna Kasashen Waje Zabe
Jun 10, 2018 14:50Jam'iyyar "National Assembly of the Democratic Republic of the Congo" ta kasar Democradiyyar Kongo ta bayyana cewa gwamnatin kasar da kuma hukumar zabe mai zaman kanta sun haramtawa yan kasar mazauna kasashen waje zabe.
-
An Kashe Wani Soja A Rikicin Yankin Masu Magana Da Turancin Ingilishi A kamaru
Jun 10, 2018 14:50Majiyar labarai daga yankunan masu magana da harshen turancin Ingilishi a kasar Kamaru ta bayyana cewa an kashe soja guda a jiya Asabar a wani harin da yan tawaje a yankin suka kai sojojin a sansanoninsu.
-
Mutum Guda Ya Mutu Biyu Suka Ji Rauni A Fashewar Bom A Garin Mubi
Jun 10, 2018 14:49Kwamishinan watsa labarai na jihar Adamawa a Najeriya Malam Ahmad Sajoh ya tabbatar da mutuwar wani yaro da kuma jikatan wasu yaran biyu a lokacinda daya daga cikinsu ya tsinci bom a wani wurin tara shari a garin Mubi daga gabacin jihar.
-
Rundunar Sojin Saman Nijeriya Ta Ce Za Ta Dakatar Da Kai Gyaran Jiragenta Waje Nan Gaba Kadan
Jun 10, 2018 06:28Rundunar sojin sama na Nijeriya ta sanar da wani sabon ci gaba da kwararrunta suka samu tana mai cewa nan gaba kadan za ta daina kai gyaran jiragen samanta kasashen waje maimakon haka za a gyara su ne a cikin gida.
-
Sojojin Kasar Libiya Sun Hallaka Wasu Jagororin Kungiyar Al-Qa'ida Uku A Garin Darna
Jun 10, 2018 06:28Sojojin kasar Libiya sun sanar da cewa sun sami nasarar hallaka wasu jagororin kungiyar ta'addancin nan ta Al-Qa'ida a garin Darna da ke gabashin kasar Libiyan.
-
Safarar Makamai Ya Kara Tsananta Rikici A Najeriya
Jun 10, 2018 02:27Karuwar cinikayar makamai na bayan fage ya kara tsanata gurbatar yanayin tsaro a Najeriya