Laberia : Tsohon Ministan Taylor, Zai Gurfana Gaban Kotun Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31606-laberia_tsohon_ministan_taylor_zai_gurfana_gaban_kotun_amurka
A wani lokaci a yau Litinin, ake sa ran gurfanar da tsohon ministan tsaron, tsohon shugaban kasar Laberia, Charles Taylor, a birnin Philadelphie na Amurka.
(last modified 2018-08-22T07:01:57+00:00 )
Jun 11, 2018 01:51 UTC
  • Laberia : Tsohon Ministan Taylor, Zai Gurfana Gaban Kotun Amurka

A wani lokaci a yau Litinin, ake sa ran gurfanar da tsohon ministan tsaron, tsohon shugaban kasar Laberia, Charles Taylor, a birnin Philadelphie na Amurka.

Ana dai zargin, Jucontee Thomas Woewiyu, da yi wa mahukuntan Amurka karya kan tarihinsa.

Kafin hakan dai ana zarginsa da aikata muggan laifuka a yakin basasar Laberia, a kungiyar 'yan tawaye ta NPFL, (National Patriotic Front of Liberia), da yake zama mamba.

A watan Mayu na 2014 ne, aka cafke Mista Thomas, a wani filin jirgin sama na Amurka bisa zargin aikata zamba, da ba daidai ba da kuma yi wa hukumar shige da fice karya, don nema wa kansa takardar zama dan kasa ta Amurka, wanda ya nuna cewa ya boye tarihinsa na zama mamba a kungiyar 'yan tawayen ta NPFL, wacce ta yi yunkurin kifar da gwamnati da karfi.

Duk da hakan kuma yana shafe dogon lokaci a kasarsa, inda har ma ya koma harkokin siyasa.