Safarar Makamai Ya Kara Tsananta Rikici A Najeriya
(last modified Sun, 10 Jun 2018 06:57:54 GMT )
Jun 10, 2018 06:57 UTC
  • Safarar Makamai Ya Kara Tsananta Rikici A Najeriya

Karuwar cinikayar makamai na bayan fage ya kara tsanata gurbatar yanayin tsaro a Najeriya

Cikin wani rahotoda ya fitar, kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa mayakan kungiyar boko haram da suka fara yiwa gwamnatin Najeriya tawaye tun daga shekarar 2009, suna samun makamai ne daga arewacin Afirka musaman kasar Libiya ta barauniyar hanya.

Rahoton ya ce a cikin watanin baya-bayan nan, gwamnatin Najeriya ta haramta rike makamai, sannan ta bukaci wadanda suke rike da makaman ba kan ka'ida da su meka su hanun jami'an tsaro ko kuma su fuskanci fishin hukuma, wannan mataki na zuwa ne a yayin da rikici manona da makiya ke ci gaba da lagume rayukan fararen hula a kasar.

Bisa wata kdiddiga da cibiyar karbar makamai ta MDD dake yankin ta yi, akwai sama da kananen makami miliyar 35 dake yawo hanun mutane a Najeriya.

A halin da ake cikin dai jami'an tsaron kasar sun samu nasarar cabke mutane da dama masu safarar makamai cikin kasar, to saidai fadin iyakar da yake kilomita 4000 da ake bi wajen shigo da makami cikin kasar na yi cikas ga jami'an tsaro wajen magance matsalar masu safarar makaman cikin kasar.