Najeriya : Buhari Na Ziyara A Marocco
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya fara wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kasar Morocco, bisa goron gayyatar da sarki Mohammed VI ya yi masa.
A yayin ziyayar da ya fara jiya Lahadi, Shugaba Buhari ya gana da sarkin na Marocco, inda bangarorin biyu suka tattauna kan batutuwa da dama da kuma kulla alaka a fannoni masu yawan gaske.
Da yammacin jiya kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar shimfida bututan iskar gas wanda zai hade kasashen yammacin Afrika.
Aikin shimfida bututun zai ratsa kasashen yammacin Afrika masu yawa, da suka hada da Najeriyar, Jamhuriya Benin, Togo da kuma Ghana, kana zai iya ketarawa har zuwa Turai.
A watan Disamba na shekara 2016 data gabata ne kasashen biyu suka amince da babban shirin na shimfida bututan iskar gas, a yayin ziyarar da Sarkin na Marocco ya kai Abuja, inda ya gana da Shugaba Buhari.