MDD : Tamowa Na Kamari A Kewayen Tafkin Chadi
Majalisar Dinkin Duniya, ta yi gargadi game da yadda matsalar karancin abinci mai gina jiki ke dada kamari a kewayen tafkin Chadi.
Kimanin yara 'yan kasa da shekara biyar, rabin miliyan ne ke bukatar agajin gaggawa da kular kiwan lafiya ta gari a yankunan dake kusa da tafkin Chadi a cewar rahoton.
Rahoton ya kuma ce matsalar ta tamowa za ta iya yin kamari, duba da yadda ake tunkarar lokacin damana da kuma yakin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin sojoji Najeriya da kuma mayakan Boko haram.
Masu bada tallafi a wadanan kasashen dake kewayen tafkin Chadi da suka hada da Najeriya, Nijar, Chadi da Kamaru, sun bayyana a wani taro manema labarai a birnin Geneva, cewa kasa da kashi guda cikin uku ne kawai na kudaden da ake bukata don shawo kan matsalar aka samu kawo yanzu.
Kakakin ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD a Abuja, Samantha Newport, ya ce duk matsalolin da ake cin karo dasu a yau, sun hada da rashin tallafi, ci gaba da kuma talauci.