Gwamnatin Kasar Congo Ta Haramtawa Yan Kasar Mazauna Kasashen Waje Zabe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31598-gwamnatin_kasar_congo_ta_haramtawa_yan_kasar_mazauna_kasashen_waje_zabe
Jam'iyyar "National Assembly of the Democratic Republic of the Congo" ta kasar Democradiyyar Kongo ta bayyana cewa gwamnatin kasar da kuma hukumar zabe mai zaman kanta sun haramtawa yan kasar mazauna kasashen waje zabe.
(last modified 2018-08-22T07:01:57+00:00 )
Jun 10, 2018 14:50 UTC
  • Gwamnatin Kasar Congo Ta Haramtawa Yan Kasar Mazauna Kasashen Waje Zabe

Jam'iyyar "National Assembly of the Democratic Republic of the Congo" ta kasar Democradiyyar Kongo ta bayyana cewa gwamnatin kasar da kuma hukumar zabe mai zaman kanta sun haramtawa yan kasar mazauna kasashen waje zabe.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto Henri-Thomas Lokondo wani dan majalisa kuma dan jam'iyyar "National Assembly of the Democratic Republic of the Congo" yana fadar haka a yau Lahadi, ya kuma kara da cewa ya fito fili kan cewa yan kasar Kongo mazauna kasashen waje a wannan karon ma ba zasu sami damar kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa mai zuwa ba. 

Lokondo ya kara da cewa a shekara 2006 da kuma 2011 ma gwamnatin da hukumar zaben kasar mai zaman kanta sun hana yan kasar ma zauna kasashen waje wadanda aka kiyasta yawansu ya kai miliyon 16 zabe. Wata majiyar ta bayyana cewa mafi yawan yan kasar kongo mazauna kasashen waje yan adawa ne da gwamnatin shugaba Josept Kabila, don suna bayyana haka a shafuffukan sadarwa na zamani da kuma zanga-zangar da suke ta gudanarwa a birnin Paris na kasar Faransa da kuma Brussel na kasar Beljika a wasu lokuta.

Ministan yan gudun hijira na kasar Kongo Mr Emmanuel Leonga ya bayyana cewa mafi yawan yan kasar ma zauna kasashen waji suna da takardun nshaida zama yan kasa na kasashe biyu.